1 Timothy 4

1To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu, 2cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta.

3Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar. 4Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba. 5Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu’a.

6Idan ka tuna wa ‘yan’uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi. 7Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah. 8Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa.

9Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum. 10Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya.

11Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa. 12Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki. 13Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa’azi, da kuma koyarwa.

14Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa’ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu. 15Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa. Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.

16

Copyright information for HauULB